JIBWIS ta aike da Ta'aziyyar Rasuwar Malam Ahmad Musa MalamMadori

Category : Current update | Sub Category : Our Activities Posted on 2020-06-21 09:28:42


JIBWIS ta aike da Ta'aziyyar Rasuwar Malam Ahmad Musa MalamMadori

Daga Ibrahim Baba Suleiman Shugaban Kungiyar wa'azin musulunci ta JIBWIS Sheikh (Dr) Abdullahi Bala Lau, ya aike da takardar ta'aziyya ga 'yan uwa da iyalai, al'ummar garin Malammadori da jihar jigawa baki daya bisa rasuwar babban limamin masallacin JIBWIS na karamar hukumar Malammadori Malam Ahmad Musa, Marigayin ya rasu bayan fama da gajeruyar jinya. Sheikh Bala Lau yace baza mu taba Mantawa da alkhairan da Malam Musa ya assasa a garin Malammadori ba, musamman a wajen dasa ilimi, da aiki tukuru wajen karantar da tauhidi tsantsa. Kafin rasuwar shi daya ne daga cikin manyan maluman JIBWIS a jihar Jigawa. Malam Ahmed Musa Mallammadori,ya rasu a asibitin Dala dake birnin Kano a jiya Juma'a. Kafin kwanciyar sa rashin lafiya a baya kadan ya yi wata huduba inda, ya bayyana cewa gidan duniya ba madauwama bane, dole kowa zai mutu dan haka ya ja hankulan musulmai da su baiwa neman lahira fiffiko domin samun rahama. Tuni akayi jana'izar sa yau asabar da misalin karfe 8 na safe a garin Mallammadori dake jihar Jigawa. Allah ya Jikan sa da rahama.