LABARAI A TAKAICE

Category : World News | Sub Category : International News Posted on 2020-07-24 02:44:28


LABARAI A TAKAICE

KPABIO YA MUSANTA KAN SA DA KAN SA KAN ZARGIN ‘YAN MAJALISA DA KARBE KASHI 60% NA KWANGILOLIN NEJA DELTA

Ministan Neja Delta Godswill Akpabio ya musanta kan sa da kan sa kan zargin da ya yi wa ‘yan majalisa da cewa su su ka karbe kashi 60% na kwangilolin hukumarraya Neja Delta NDDC. Akpabio ya baiyana haka a wasikar da ya aikawa majalisar wakilai da ke zama amsa ga bukatar kakakin majalisar Femi Gbajabiamila ta ya fito da sunayen wadanda su ka karbi kwangilolin.

In za a tuna lamarin ya samo asali ne daga zaman kwamitin majalisa da ke biciken kashe sama da Naira biliyan 82 a cikin wata 3 a hukumar, inda Akpabio ya yi zargin. Musanta kan sa da Akpabio ya yi ka iya jefa ayar tambaya kan gaskiya ko rashin gaskiyar sa da yiwuwar neman karkatar da binciken ne ya jawo maganganu daban-daban kan lamarin.*

Hakanan wasu masu sharhi na cewa ta ka yiwu an bukaci Akpabio ya boye sunayen don ka da a cigaba da tona asirin wasu mutane.

ZA MU CIGABA DA BINCIKEN FARFESA PONDEI IN YA MURMURE DAGA SUMAR DA YA YI-DAN MAJALISA SHEHU KOKO

Dan majalisar wakilan Najeriya Shehu Muhammad Koko ya ce kwamitin su na majalisar wakilai da ke bincken zargin badakalar biliyoyin Naira a hukuamr raya Neja Delta, zai cigaba da binciken shugaban hukumar Farfesa Kemebradikumo Pondei wanda ya dibibice a gaban kwamitin. Koko ya kara da cewa da zarar an samu tabbacin warwarewar Pondei daga likitoci, za su gaiyato shi ya dawo don kammala yi ma sa tambayoyi.

Sai dai Koko ya ce ba shi damar zaiyana suma da Pondei ya yi bayan yi ma sa tambayar batar kudi, da gaske ne ko kuwa waskiya ce kawai. Tambayoyi biyu ne da Koko ya yi ma sa na kashe fiye da miliyan 600 ga daya daga kwangiloli ta sanya Pondei shidewa ko sumewa.

BA MAMAKI ZIYARAR BAMAKO YA SA SHUGABA BUHARI SANYA KARIYAR FUSKA A KARO NA FARKO

Da alamu ziyarar shugaba Buhari zuwa Bamako, Mali ta sa shugaban daura kariyar fuska a karo na farko da a ka gan shi da kariyar a cikin jama’a. Shugaba Buhari na daga cikin shugabannin duniya da ba a ganin su da kariyar don rashin ingancin bayanin tasirin sa ko muni da wadanda su kan sanya shi ke yi. Hakanan mutane kan taba kariyar don rashin sabo da ita kazalika ta kan toshe numfashin wasu mutane.

Shugaba Buhari da wasu shugabannin Afurka ta yamma sun sauka a Bamako don sulhunta shugaba Boubacakr Keita da masu zanga-zangar neman ya sauka daga mulki. Mali na daga kasashen da ke fama da ‘yan ta’adda da kuma a ke fargabar ballewar rikici a kasar ka iya shafar yankin Afurka ta yamma gaba daya.

AN SAMU NASARAR AIKIN TIYATA KAN MAFITSARAR SARKI SALMAN A ASIBITIN SARKI FAISAL A RIYADH

Gidan sarautar Saudiyya ya ba da labarin nasarar aikin fida da a ka yi wa sarki Salman kan mafitsarar sa a asibtin Sarki Faisal da ke Riyadh. Sarkin wanda ya ke kwance a asibitin a ‘yan kwanakin da su ka wuce, ya samu ciwo a mafistsarar sa da ya sanya samun lokaci har a ka gudanar da fidar. Sarkin zai kara zama na ‘yan kwanaki a asibitin bisa shawarin tawagar likitocin da ke duba shi.

Ibrahim Baba Suleiman
Jibwis Media & Publicity
media@jibwisnigeria.org
*l03-Dhul Hajji-1441
24-July-2020